Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Sokoto na bayyana cewar tsohon gwamnan jihar Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya bayyana takaicinsa kan kashe-kashen al’umma da ‘yan bindiga ke yi a yankin, yana mai kira ga Shugaban ?asa Muhammadu Buhari da “ya ji tsoron ha?uwarsa da Allah”.
Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne cikin wata hira da BBC Hausa kwanaki ka?an bayan ‘yan fashin daji sun ?ona wata motar bas ?auke da mutum kusan mutum 30 a cikinta a ?aramar Hukumar Sabon Birni ta Sokoto.
Bafarawa ya ce: “Wajibi ne Buhari ya bi al’umma a zauna a tattauna kamar yadda ya bi su gida-gida lokacin da yake neman ?uri’a, saboda mu taimaka masa wajen ha?uwarsa da Allah.”
