A daidai lokacin da jam’iyyar APC mai mulkin ke shirin gudanar da za?en shugabaninta a matakin jiha, bisa ga dukkan alamu wata babbar ?araka ta kunno kai tsakanin manyan ?a?an jam’iyyar a jihar Kano.
?arakar na da nasaba da zargin da jiga-jigan jam’iyyar suke yi wa gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da yin babakere tare da yin gaban kansa wajen yanke hukunci a kan al’amuran da suka shafi jam’iyyar.
A ranar Talata da daddare, wasu ?usoshin jam’iyyar ciki har da tsofoffin gwamnan jihar ta Kano, Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Kabiru Gaya da ?an majalisar dattijai Sanata Barau Jibrin da ?an majalisar wakilai, Sha’aban Sharada da wasu manyan ?a?an jam’iyyar suka gudanar da taro inda suka yanke shawarar cewa dole ne shugabancin jam’iyyar APC ya taka wa Gwamna Ganduje birki kafin lamura su dagule.
?aya daga cikin jagororin APC a Kano wanda yake cikin taron da aka yi a ranar Talata ya shaida wa BBC cewa sun yanke shawarar ganawa da shugaban ri?o na jam’iyyar APC na ?asa, Gwamna Mai Mala Buni domin bayyana masa korafe-korafensu kafin lokacin ya ?ure.
Bayanai sun nuna cewa a yammacin Laraba ne za a gudanar da taron tsakanin ?usoshin APC na Kano da shugaban na ri?o.
Jigon na APC ba ya son a bayyana sunansa har sai sun kammala taronsu da Gwamna Buni, kafin su fitar da sanarwar da za su bai wa manema labarai.
Ya ?ara da cewa “yadda Ganduje ke jagorancin APC a Kano, ba ya neman shawarar kowa. Shi ka?ai yake yanke hukunci ba ya neman shawara.”
Ba wannan ba ne karon farko da jiga-jigan APC a Kano suke nuna ?an yatsa tare da zargin gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da yin babakere wajen rarraba mu?aman siyasa a jihar.
Wasu majiyoyi sun ce ministan tsaro, Janar Salihu Magashi ritaya wanda bai halarci taron da aka yi ba a jiya, shi ma ya nuna goyon bayansa ga taron.
Jim ka?an bayan da aka gudanar da za?en shugabannin maza?u na APC a Kano a ?arshen watan Yuli, wasu jiga-jigan APC suka bayyana cewa ba a bi ka’ida ba wajen gudanar da zaben.

‘Martanin ?angaren Ganduje’
Shugaban ri?o na jam’iyyar APC a Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ya shaida wa BBC cewa sun ji mamakin wannan taron da aka yi.
Ya bayyana cewa su ba su da wata damuwa game da wannan taron kuma za?e za a yi a ?arshen mako kuma duk wanda ya samu nasara za a ba shi dama ya ja ragamar jam’iyyar a matakin jiha.
“Jam’iyyar APC ha?aka ce, kuma kowanne ?angare an ba shi mu?ami daidai da su bisa adalci,” in ji Abbas.
Shugaban na ri?o ya ?ara da cewa sun ji mamaki yadda Malam Ibrahim Shekarau ya halarci taron da aka yi a ranar Talata.
A watannin da suka wuce ma sai da wani ?usa a jam’iyyar APC, Dan Balki Kwamanda ya caccaki salon jagorancin APC a Kano inda ya ce ba za su zura ido a dunga kama-karya ba a cikin jam’iyyar.
