Da Dumi-Dumi: Shugaban Sarakunan Taraba Ya Mutu

Marigayin, wanda shi ne ‘Sarkin Jukunawa’ ya mutu yana da shekara 84 a duniya.

Wakilinmu ya jiwo cewa Sarkin mai daraja ta daya kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Taraba ya mutu ne ranar Asabar a fadarsa dake Wukari bayan yayi fama da rashin lafiya.

Dokta Shekarau Agyo dai ya dare kan karagar mulki ne a watan Agusta na shekarar1976, ya shafe kimanin shekara 45 kenan a kan gadon mulki.

Wata majiya daga gwamnatin Jihar ta shaida cewa a al’adance, Gwamnan Jihar ne kawai zai iya bayar da sanarwar mutuwar Sarkin a hukumance bayan an kammala wasu al’adu kamar yadda yake kunshe a al’adun ’yan kabilar ta Jukun

Related posts

Leave a Comment