Katsina: An Kama Inyamuran Dake Safarar Muggan Kwayoyi Ga ‘Yan Bindiga

Rundunar yan sandan Najeriya dake a jihar Katsina ta bayyana samun nasarar cafke wasu mutane su uku da laifin kaima yan bindiga kwayar allurar ‘fenta’ watau Pentazocin a turance a daji.

Wadanda aka kaman sun hada da wasu Inyamurai guda biyu da Patience da kuma Chima wanda shi mai sana’ar saida magunguna ne watau Kemist.

Sauran sun hada da wata bafullatana mai suna Hafsat wadda mata ce ga daya daga cikin shugabannin yan bindiga a dajin na Katsina mai sune Sheman daji da kuma wata Maimuna da ake nema a jallo.

Da yake gabatar da su a gaban yan jarida, kakakin rundunar yan sandan na Katsina, SP Gambo Isah ya ce yan banga ne suka kama Hafsat da allurorin kafin daga bisani su mika su ga jami’an tsaro.

Ya kara da cewa ita Hafsat din ta bayyana ma su cewa Patience ce tayi mata hanya ta kai ta wurin shi Chima wanda ya saida mata alluran har guda 150 akan kudi Naira dubu 30.

Ya kama kara da cewa yanzu haka suna kan bincike da zaran sun kammala za su gurfanar da su gaban kotu.

Related posts

Leave a Comment