Na Rantse Bidiyon Karbar Dala Shiri Ne – Ganduje

Lokacin da gwamnan ke amsa tambaya cikin shirin a fada a cika na BBC Hausa dangane da Bidiyon karbar Dala wanda aka nuna shi yana cusawa a aljihu ya ce wannan bidiyo da aka fitar ba gaskiya ba ne, kuma ya ce ana bincike a kai kuma za a dauki mataki kan duk wanda ke da hannu.

Ya ce wadanda suka yi bidiyon sun yi ne a matsayin ma?ar?ashiya domin hana shi shiga za?e, sai dai ba su ci nasara ba.

Wannan layi ne

A ?angare guda kuma gwamnan ya ce gwamnatinsa ta aiwatar da ayyuka da yawa a jihar, amma kuma a cewarsa har yanzu akwai sauran matsaloli da yawa.

Yana mai shaida cewa gwamnatinsa ta gudanar da ayyuka wadanda za a rin?a tunawa da shi sama da shekara 100 masu zuwa

Ayyukan da gwamnan ya kafa hujja da su, su ne manyan gadoji da ya gina a birnin Kano, da kuma asibitin Muhammadu Buhari, wanda ya ce an sanya wa kayan kiwon lafiya na zamani.

Related posts

Leave a Comment