Ranar ‘Yancin Kai: Mun Shirya Tsaf A Jihar Adamawa – Rundunar ‘Yan Sanda

Rundunan yan sandan jahar Adamawa tace ta kimtsa tsaf domin daukan dukkanin matakai da suka dace domin ganin angudanar da bkin samun yancin kai cikin lumana ba tare da wata matsalaba.

Kwamishinan yan sandan jahar Adamawa CP Muhammed Ahmed Barde ne ya baiyana haka a wata sanarwa dauke da sanya hanun kakakin rundunan D S P Suleiman Yahaya Nguroje wanda aka rabawa manema labarai a yola,

Kwamishinan ya umurci dukkanin manyan jami an yan sandan dake fadin jahar da su tabbata sun tura Jami an tsaro a wuraren da za a gudanar da bukuwar ranan samun yancin wanda za ayi gobe indan Allah ya kaimu.

Kwamishinan ya kuma taya gwamanan jahar Adamawa Ahmdu Umaru Fintiri tare da al umma jahar Adamawa murnan zagayowar ranan da Najeriya ta samu yancin kanta.

Ya kuma shawarci al umman jahar ta Adamawa da sukasance masu baiwa Jami an tsaro hadin kai da goyon baya domin acewarsa hakan zaitaimaka wajen kawar da aikata laifuka a tsakanin al umma.

Related posts

Leave a Comment