Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na nuna cewa da Alama Gwamnan Jihar Farfesa Babagana Umara Zulum baya tare da Gwamnonin Arewa a Game da Fitar da Dan takarar Shugaban kasa, a shekarar za?e ta 2023.
Gwamna Zulum ya bayyana cewar, matukar Obasanjo zai mika mulki ga Arewa yayinda ya kammala Mulki, duk kuwa da cewar daga Kudancin Nigeria ya fito, to bai kamata mu idonmu ya rufe da son mulki ba,
Ya kamata muyi abinda yake shine adalci, kuma ya zamana shine zai hada kan kasar gabadaya. Amma cewar Arewa ta cigaba da Mulki ba abinda Hakan Zai Haifar Sai rarrabuwa kan ‘yan kasa.
Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da manema labarai da yayi, jim ka?an bayan halartar taron Gwamnonin Arewa da ya gudana a Kaduna.
