Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kwamitin da aka kafa domin ya yi bincike a kan hadarin jirgin saman da ya kashe tsohon hafsun sojojin kasa, Ibrahim Attahiru ya gama aikinsa, kuma har ya mika Rahotonsa.
An ruwaito cewa kwamitin ya gabatar da rahoton farko ga rundunar sojojin saman Najeriya. Rahoton wannan bincike ya bankado wasu muhimman abubuwa 27 kan faduwar jirgin.
Mai magana da yawun bakin rundunar sojojin sama, Edward Gabkwet da kakakin AIB, Tunji Oketunbi sun bayyana haka a wani jawabi da suka fitar. Rahoton binciken ya fito ne bayan sama da watanni uku da mutuwar hafsun sojojin kasa, Laftana-Janar Attahiru Ibrahim da wasu sojoji a Kaduna.
Gutsuren jawabin da aka fitar “Bayan kusan watanni uku ana bincike, Shugaban AIB, Injiniya Akin Olateru FNSE ya gabatar da rahoton abin da ya faru ga shugaban hafsun sojojin sama, Air Marshal I. Amao, a yau, ranar 15 ga watan Satumba, 2021, a ofishinsa da ke hedikwatar NAF a Abuja.”
“An kasa rahoton zuwa bangare-bangare; bayanan da aka samu wajen binciken, abin da aka fahimta daga bayanan da aka samu, da kuma kammala wa, wanda ya kunshi abin da aka gano da shawarwari.”
“A somin-tabin binciken, an gano abubuwa 27 da shawarwari 8 da ya kamata ayi gaggawar dauka.” Wannan ne karon farko da AIB suka yi irin wannan bincike Kwamitin na AIB ne aka ba dama ya gudanar da wannan bincike duk da cewa bai da hurumin ya gudanar da bincike game da hadarin jiragen sojojin kasa.
Kamar yadda jawabin ya bayyana, ana sa rai rahoton karshe zai kunshi cikakken bayanin abin da ya faru da kuma matakan da ya kamata a dauka nan gaba.
