Boko Haram Sun Bude Sansani A Jihar Kaduna – DSS

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta nemi hukumomin tsaro a Kaduna da su kasance cikin shirin ko ta kwana kan yiwuwar kai hare-hare, a sassa daban daban na fa?in ?asar.

Sanarwar ta bayyana cewa shugabanni da dakarun kungiyar ‘yan ta’adda na Boko Haram sun koma wani daji a Kudancin Kaduna bayan barin su Dajin Sambisa.

A cikin wata sanarwa da jaridar Peoples Gazette ta gani, an ce yan ta’addan sun kaura daga dajin Sambisa a jihar Borno zuwa dajin Rijana da ke karamar hukumar Chikun ta Kaduna.

“Wani babban mayakin Boko Haram, Ibrahim (FNU) tare da sojojinsa” suna ?aura don komawa cikin takwarorinsu” karkashin jagorancin wani Adamu Yunusu (wanda ake kira Saddiqu)”. Don haka, DSS, ta umarci jami’an tsaron Najeriya da jami’an NSCDC da su tsaurara tsaro a yankunan da aka ambata da kuma kewaye, inda ya kara da cewa yakamata ta sanya jami’an ta cikin shiri da bayar da rahoto yadda ya kamata.

Related posts

Leave a Comment