Ina Fatan Rasuwar ?ana Ta Kawo ?arshen Matsalar Tsaro A Najeriya – Na’Allah

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Sanata Bala Ibn Na’Allah, wanda miyagu suka halaka babban dan shi Abdulkareem a gidan shi da ke Malali jihar Kaduna, ya ce rayuwar dan shi ba ta fi ta kowanne dan Najeriya ba, duka ?aya suke kwanan shi ya ?are.

A wata takarda da ya fitar a ranar Litinin, Na’Allah ya bayyana fatansa na cewa ta yiwu mutuwar dan sa ta taka babban rawa wurin shawo kan matsalar tsaron dake addabar Najeriya musamman yankin Arewacin kasar.

Sanata Na’Allah wanda baya kasar Najeriya yayin da lamarin ya auku, ya ce wadanda suka kai wa dan sa farmaki ba dauke suke da bindigogi ba. Sun samu damar shiga gidansa ne ta rufi kuma suka shake shi.

A matsayin mu na danginsa, mun bar komai a hannun Allah wanda tuni muka fawwala masa komai domin ya bamu hakurin jure rashin Abdulkareem a tare da mu. Ko daga kira, sakonni da kuma ziyarar da muke ta samu, mun godewa Allah da irin wannan kaunar da jin kai da aka nuna gare mu,”

Na’Allah, sanatan da ke wakiltar Kebbi ta kudu, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan lamurran sojin sama, ya kara da cewa: Kwamishinan ‘yan sanda ya ba da umarnin a binciko wadanda suka kashe dan sanata Muna tabbatarwa da jama’a cewa mun matukar jin kaskanci ta yadda aka kashe shi, amma kuma mun saka tawakkali a lamarin.

Za mu cigaba da jajircewa tare da hakurin wannan rashin da muka yi na babban jakadan dangin mu da muke alfahari da shi. Muna fatan mutuwarsa za ta taka babbar rawa wurin shawo kan matsalar da kasar mu ke fuskanta.

Ya mika godiyarsa ga ‘yan sanda da gwamnatin jihar Kaduna kan daukin da suka kai tare da fatan rahama ta har abada ga Abdulkareem. An ruwaito cewa, matukin jirgin mai shekaru 36 a duniya shi ne babban dan Na’Allah wanda aka ga gawarsa a gidansa da ke titin Umar Gwandu a Malali, daya daga cikin kasaitattun anguwannin Kaduna.

Related posts

Leave a Comment