Kano: An Gafarta Wa Amaryar Da Ta Yi Wa Mijinta Yankan Rago

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Kwamitin gyara da rage yawan mutane a gidajen yarin jihar ya saki Rahma Husseini, amaryar da kotu ta kama da laifin kashe mijinta a jihar Kano shekaru bakwai da suka gabata.

Kwamitin karkashin jagorancin Alkali Ishaq Bello, ya taimaka wajen sakin wasu fursunoni 30 daga gidajen yari daban-daban a ranar Juma’a, domin rage cunkoso a gidan yarin.

Idan zaku tuna cewa a 2014, an damke Rahma Hussein, da laifin kashe mijinta kwana daya bayan daurin aurensu. Alkali R.A Sadik a 2018 ya bada umurnin jefa ta kurkuku amma zuwa lokacin da gwamnan jihar yaga dama saboda an yi mata auren dole ne kuma an yi mata aure tana yar shekara 16.

Tun daga lokacin, babu gwamnan da ya waiwayi lamarin sai yanzu da kwamitin ya kai ziyara gidajen yari don rage yawan fursunoni.

Kakakin gidajen yarin Kano, Musbahu Kofar-Nassarawa, yace an saketa ne bisa shawarar jami’an gidan yarin saboda tana da halayya na kwarai.

A cewarsa, kwamitin ya ba gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, shawara ya duba lamarin a yafe mata tun da Alkali ya jingine hukuncinta ne da ganin daman gwamna. Yace gwamnan ya karbi shawarar kuma ya yafe mata.

Bayan saketa, Rahma Hussein, cikin farin ciki ta godewa kwamitin, gwamna Ganduje, da jami’an gidan yarin da suka taimaka wajen sakinta. Rahama cikin hawaye tace: “Ina godiya ga wannan kwamitin, Allah ya saka muku Jami’an Kurkukun da suka bada shawaran sakeni, Allah ya saka muku.”

Related posts

Leave a Comment