Ba Za Mu Hukunta Tubabbun ‘Yan Boko Haram Ba – Gwamnatin Tarayya

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin da zai hanata kashe tubabbun yan ta’addan Boko Haram wa?anda suka mi?a wuya ga dakarun soji.

Ministan ya?a Labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana hakan a hirar da yayi da kamfanin dillancin labarai NAN ranar Juma’a, 20 ga Agusta, 2021 a Abuja.

“Kawai ba za’a iya harbesu ba saboda akwai dokokin duniya da suka bada kariya ga fursunonin yaki. “Abinda Sojoji ke yi shine idan suka mika wuya, suna daukan sunayensu domin tabbatar da cewa da gaske suke sannan a mayar da su cikin al’umma.”

Anata Bangaren Kungiyar kare hakkin musulmai ta MURIC tayi kira ga gwamnatin tarayya da hukumar sojin Najeriya akan shiryawa da tubabbun mayakan Boko Haram da ISWAP.

MURIC ta bayar da wannan shawarar ne a wata takarda da ta saki a ranar Alhamis inda tace ya kamata a kula da tubabbun ‘yan ta’addan tamkar ‘yan uwa wadanda suka bata aka gansu.

Amma Kungiyar Arewa Consultative Forum, ta yi watsi da maganar yafewa yan ta’addan Boko Haram da suke mika wuya ga gwamnati da kuma sakinsu.

Shugaban kungiyar na kasa, Cif Audu Ogbeh, ya ce wajibi ne a hukunta yan ta’addan kan laifukan da suka aikata kan yan Najeriya.

Related posts

Leave a Comment