Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamna Bello Matawalle na jihar ya ce jihohin Najeriya su dauki matakin sulhu da lalama da ‘yan Bindiga dake Jihohin nasu, domin shawo kan matsalolin tsaro da sauran ayyukan ashsha dake addabar Najeriya.
Gwamna Bello Matawalle ya kara da cewar sulhu da aka yi da ‘yan bindiga a Jihar Zamfara ya kawo masu zaman lafiya, wanda suke alfahari da ita, kuma suke fatan wannan nasara da suka samu ta fadada zuwa sauran yankunan kasar.
Da yake magana da kamfanin dillacin labarai na kasa NAN, gwamnan jihar Zamfara ya bada shawarar ayi koyi da matakin da ya dauka wajen tsare rayuka da dukiyoyi jama’a, domin tabbas sun yi sun gani.
“Kamar yadda na ambata a baya, sha’anin rashin tsaro ba matsalar wasu rukunin mutane kadai ba ce, aikinmu ne mu duka.” “Ko kai jami’in tsaro ne, ko mazaunin gari ko gama-gari, muhimmin abu shi ne, duk mu hadu, mu dauka wannan matsalarmu ce, mu yi kokarin shawo kanta.”
“Bayan na zama gwamnan jihar Zamfara, na san cewa a kwanakin 100 na farko da na yi, mun ci nasarorin da ba a iya samu a shekaru shida da suka wuce ba.” “Mun cin ma wannan nasara ne saboda na kira kowa, na zauna da shi. Mun tattauna da masu ruwa da tsaki; ‘yan siyasa, sarakuna, shugabanni da jami’an tsaro.” “Muka hada karfi da karfe, shiyasa muka kawo maganar ayi zaman sulhu da lalama da ‘yan bindiga, kuma hakan ya kawo mana nasarori sosai a jihar (Zamfara).”
“Kowace jiha tana bukatar ta dauki irin wannan tsari na samar kwanciyar hankali. Idan muka hadu, muka dauki matsaya daya, na yi imani zai yi mana amfani.”
