Rahotanni daga Jihar Bauchi na bayyana cewar Gwamna Bala Muhammed na jihar, yace iyalansa da abokanan arziki sun matsa mai lamba ya nemi takarar shugabancin kasa a za?en 2023 dake tafe, wanda hakan ya jefa shi cikin nazari da tunani akai.
Gwamnan ya fa?i haka ne yayin da ya karbi bakuncin kungiyar matasan arewa da kungiyar direbobi (NURTW) da wasu kungiyoyi a gidan gwamnati dake Bauchi, ranar Alhamis.
Da farko gwamnan ya nemi masu kiraye-kiraye da kunguyoyi su bashi mako uku yayi nazari tare da tuntubar wasu mutane kan ya fito takarar ko kada ya fito.
Sai dai bayan makwanni ukun da ya nema sun shude, gwamna Muhammed ya sake neman a bashi wasu mako ukun domin yanke hukunci na karshe. A halin yanzun, Gwamnan jihar Bauchi ya sake neman karin lokaci domin yanke hukunci, ranar Alhamis.
“Tun a baya abokanaina sun matsamun lamba na nemi takara, iyalaina suka nuna goyon bayansu. Jam’iyyar PDP reshen jihar Bauchi ta roke ni na nemi takarar nan.” “Har yanzun muna cigaban da yin shawara ne.
A baya da kuka zo na fa?a muku akwai bukatar in yi shawara.” “Hakazalika a yanzun ma zan nemi alfarmar ku bani wani lokaci, akwai bukatar nazari sosai kan lamarin ne shiyasa muke cin lokaci. Ina mai baku hakuri.”
Muhammed ya gode wa ha?akar kungiyoyin baki ?aya bisa ganin cancantarsa da suka yi kuma suka nemi ya fito takara, Ya kara da cewa wannan ba shine karo na farko da aka bukace shi da ya fito takarar shugaban ?asar Najeriya ba.
