Ku Taimaka Ku Daina Satar Dalibai – Rokon Gwamnatin Tarayya Ga ‘Yan Bindiga

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gwamnatin Tarayya ta bakin karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, tayi kira ga ‘yan bindiga da su hakura kuma su taimaka su daina sace daliban makarantu.

Ministan yayi wannan kiran ne yayin da ya bayyana a shirin siyasarmu a yau ta gidan talabijin na Channels, yayin da aka tambaye shi kan tsokacin da zai iya yi kan dalibai uku na makarantar Bethel Baptist da ‘yan bindigan suka sako a jihar Kaduna.

“Ina farin ciki, irin wadannan labaran nake son ji a kowacce rana. Su dawo mana da yaranmu. Ina yi wa yaran farin ciki tare da iyayensu, amma ina roko kuma zan cigaba da roko, don Allah’yan Bindiga su hakura haka su daina sace mana dalibai.

“Na je Katsina domin in roki dakarun sojinmu dake tuka jiragen sama zuwa wuraren nan da su dage kuma suna kokarin bibiyar masu garkuwa da mutane. Amma kuma ina rokon ‘yan bindigan da duk wanda suke jin maganarsa, da su taimaka su bar mana yaranmu.

A halin yanzu muna da matsaloli daban-daban, daga Kagara zuwa Jangebe, duk sun hana yara zuwa makaranta. Wannan bai dace ba. Rashin tsaro babbar matsala ce dake hana karatu.

Ina farin cikin dawowar wadannan ukun gida kuma zan yi farin ciki idan sauran suka dawo Minista ya tabbatarwa iyaye za a ceto ‘ya’yansu Nwajiuba ya kara da tabbatarwa da iyayen dalibai cewa gwamnati za ta yi duk abinda ya dace wurin tabbatar da an sako yaransu da aka sace.

Sama da dalibai 900 a halin yanzu ke hannun ‘yan bindiga bayan sun sace su daga makarantunsu. Duk da tabbacin da gwamnatin tarayya ta cigaba da baiwa jama’a na bada kariya, miyagu sun cigaba da gallazawa jama’a.

Related posts

Leave a Comment