Saudiyya Ta Tsaurara Dokar CORONA

Gwamnatin Saudiyya ta ce daga ranar Lahadi ta 1 ga watan Agusta babu wanda zai shiga kantinan zamani ko kuma wuraren sana’o’i ko motar haya ko ofisoshin gwamnati sai wanda aka yi wa rigakafin korona.

Ma’aikatar cikin gidan kasar ce ta bayyana hakan, tana cewa dole kowa ya fito a yi masa rigakafin ko a wanne yanki yake na masarautar.

Saboda fargabar sabuwar dokar, an karo yawan rigakafin kuma ana samun dogayen layuka a Riyadh da sauran wurare.

Adadin wadanda aka yi wa rigakafin cikakkiya a Saudiyya ba shi da yawa idan aka kwatanta da makonta na yankin Golf.

Tun daga farkon bullar annobar, masarautar na ?aukar tsauraran matakan da suka kamata – wadanda suka shafi dakatar da aikin Hajj har saubiyu.

Ko a makon jiya, sai da aka yi wa mutane gargadi kan cewa za su iya fuskantar haramcin tafiya idan suka shiga Saudiyya daga kasashen da Saudiyyar ta hana zuwa

Related posts

Leave a Comment