Malaman Kano Sun Nesanta Kansu Da Batun Haramtawa Mata Tuki

Rahotanni daga birnin Kano na bayyana cewar Majalisar Malaman Jihar ta fito fili ta nesanta kanta daga wata maganar da ake ya?awa cewa wai tana kira da bada shawara akan haramtawa Mata tukin Mota a fadin Jihar.

Mai magana da yawun su fitaccen Malamin addinin Musulunci dake Jihar Sheikh Dr Sani Umar Rijiyar Lemu ya Bayyana hakan a cikin wata takardar sanarwa da fitar, kuma aka rabata ga manema labarai.

“Mun ga wani labarin karya da ake yadawa cewa, wai wasu malamai a Kano, daga cikinsu har da ni, sun gabatar wa da Gwamnatin Kano kudurin hana mata tukin mota a Kano”. “Wannan labari, bisa dukkan alamu, wasu ne daga cikin Shi’a wadanda ba su ji dadin titsiyen da aka yi Abduljabbar ba suka tsara shi, suke kuma yadawa.” A yi watsi da wannan labari domin tsatsuniya ne ba gaskiya ba. Allah ya kare mu sharrin makiya Allah. Amin.
.

?? Dr Muhammad Sani Umar R/Lemo

Related posts

Leave a Comment