Saudiyya Ta Haramta Wa Kasashe 13 Yin Umrah

Rahotanni daga Kasar Saudiyya na bayyana cewar Hukumar dake kula da masallatai biyu masu tsarki a kasar Saudiyya ta bayyana sunayen wasu kasashe 13 da ba’a amince su je aikin umrah da aka bu?e kwanan nan ba.

Wannan na kunshe ne a wata takarda da shafin Haramain Sharifain na dandalin sada zumunta facebook ya fitar ranar Laraba.

A jikin takardar, Saudiyya ta bayyana cewa an ?auki wannan matakin ne saboda karuwar masu harbuwa da cutar COVID19 a kasashen.

Hakanan kuma Saudiyya tace ba wai aikin Umrah ka?ai aka hana mutanen wa?annan ?asashen ba harda shiga ?asa baki ?aya.

Kasashen da wannan hanin ya shafa sun ha?a da Afghanistan, Argentina, Brazil, Masar da Habasha Sauran sune, Indiya, Indonesia, Lebanon, Pakistan, Afirka Ta Kudu, Turkiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa.

Wani ?angaren takardar, yace: “Duk mutanen da suke son shiga Saudiyya da suka je wadannan kasashen, sai sun killace kansu na makwanni 2, kafin su fara batun zuwa kasa mai tsarki.”

“Ma’aikatar cikin gida na cigaba da bibiyar kasashen duniya kan ya?uwar cutar korona, kuma za’a iya ?ara wasu kasashen nan gaba ba tare da sanarwa ba.”

Saudiyya ta shawarci musulmin duniya da su ziyarci ofishin jakadancinta dake kasashen su domin sanin ko kasar su na cikin hanin kafin su ?aura ?amarar tafiya.

Related posts

Leave a Comment