Kano: Majalisa Ta Bada Shawarar A Kama Rimin Gado

Majalisar dokokin Kano ta bu?aci a gaggauta kora da cafke shugaban hukumar korafe-korafe da ya?i da rashawa na jihar da aka dakatar Muhiyi Magaji Rimin-Gado.

Kamfanin dilancin labaran Najeriya wato NAN ya ce majalisar ta yanke wannan shawarar ne bayan wani zama da ta yi ?ar?ashin jagoranta, Hamisu Chidari, a ranar Litini.

A lokacin gabatar da rahoton, shugaban kwamitin wucin-gadi da aka na?a domin bincike akan zargin da ake yiwa Muhiyi, Musa Gama na jam’iyyar PDP ya shaida cewa mambobin kwamitin mai ?unshe da mutum 12 sun kammala bincikensu da kuma gabatar da bukatu biyar.

Gama ya ce daga cikin shawarwari da suka bayar harda kora Muhiyi, wanda yanzu haka ke fuskantar dakatarwa, a cafke shi da kuma gurfanar da shi.

Sannan rahoton ya bukaci a kafa kwamitin da zai bincike ayyukan ku?i da hukumar ta gudanar daga shekara ta 2015 zuwa yanzu

Related posts

Leave a Comment