Duba Lafiya: Buhari Ya Garzaya Birtaniya Yau

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi Landan domin a duba lafiyarsa, kuma ana sa ran zai koma kasar a mako na biyu na watan Agustan gobe.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugana Femi Adesina ya fitar ya ce Buhari zai bar Najeriya ne a ranar Litinin 26 ga watan Yulin da muke ciki.

Gabanin haka Buhari zai halarci wani taro na duniya kan shirin tara kudi don inganta ilimi a kasashen duniya tsakanin shekarun 2021 zuwa 2025.

Taron wanda Firaiministan Burtaniya Boris Johnson zai karbi bakunci da kuma shugaban Kenya Uhuru Kenyatta zai samu halartar shugabannin kasashen da masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi da shugabannin matasa domin hada kai wajen samun mafita kan harkokin ilimi.

Kuma zai bayar da dama ga shugabanni na tsara yadda za a kawo sauyi a tsarin ilimi a kusan kasashe 90 da yankuna da dama cikin shekaru biyar.

Makalolin da za a gabatar a yayin taron za su mayar da hankali kan: Karfin ikon da ilimi ke da shi, tattaunawa tsakanin wadanda suka yi fice, kawo sauyi kan tsarin ilimin ‘ya’ya mata, zuba kudi da kuma farfado da harkokin ilimi, mai da hankali kan kawo sauyi a tsarin ilimi nan da shekatra biyar da dai sauransu.

Buhari zai yi wata tattaunawa ta musamman da Firaiministan Burtaniya Boris Johnson a gefen taron.

Related posts

Leave a Comment