Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamnatin jihar ta sanya ranar da za a fafata mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da wasu malamai a jihar domin bayyana gaskiya.
Kwamishinan harkokin addinai na jihar Muhammad Tahir Adamu wanda ake kira Baba Impossible ne ya bayyana haka ranar Alhamis a tattaunawarsa da sashen Hausa na BBC.
Ya ce za a gudanar da mukabalar ce ranar Asabar 10 ga watan Yuli a Hukumar Shari’a dake birnin na Kano.
A cewarsa tuni ya mika takardar gayyatar yin mukabalar ga Abduljabbar da malaman da za su fafata da shi. Kwamishinan ya bayyana haka ne kwanaki kadan bayan shugabannin zauren hadin kan malaman Kano suka zargi Gwamnatin jihar da “jan kafa” game da zaman tuhumar da ake yi wa Sheikh Abduljabbar a kan zargin cin zarafin Manzon Allah (SAW) da Sahabbansa.
Da ma dai Sheikh Abduljabbar ya bayyana dakatarwar da gwamanatin ta yi masa na yin wa’azi da rufe masallacinsa da cewa “zalunci ne”.
A baya, shugaban malamai na arewa maso yamma, Sheikh Ibrahim Khalil, ya sanar da cewa kima da darajar Malam Abduljabbar Kabara basu kai ga malamai su yi masa gangamin taron dangi ba.
Sheikh Khalil ya sanar da hakan ne yayin tattaunawa da manema labarai kan abinda ke faruwa tsakanin Abduljabbar da gwamnatin Kano.
Tun farko dai Ganduje ya haramtawa malamin yin wa’azi sakamakon zargin da da ake yi da bayar da wasu fatawoyi da suka sabawa koyarwar addini.
