Kungiyar kiristocin Nigeria (CAN) da kuma kungiyar marubutan kare hakkin dan Adam (HURIWA) sunyi kira ga gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da ya sauka daga kujerarsa ta gwamna saboda ta’azzarar matsalar rashin tsaro a jihar.
Kiran na su ya biyo bayan yadda gwamnan ya gaza a matsayinsa na shugaban hukumomin tsaro a jihar da kuma kin yin sulhu da yan bindiga masu garkuwa da mutane jihar.
A Jiya Litinin dalibai 26 yan bindiga suka yi garkuwa da su a makarantar Bethel Baptist, Maraban Rido, Karamar hukumar Chikun a Jihar Kaduna. Da take tabbatar da faruwar lamarin jiya, rundunar yan sandan jihar ta ce jami’an tsaro suna bibiyar yan bindigar.
Kungiyoyin HURIWA da CAN sun ce El-Rufai ya gaza Shugaban CAN, reshen Kaduna, Rev. Joseph Hayab, wanda babban malamin cocin Baptist ne, yayi bayanin cewa daliban dake zaune a dakunan kwana kafin ayi garkuwar 180 ne, ya kara da cewa: ‘mun kirga su da safiyar nan (Litinin) kuma ba a ga mutum 174 ba.’ Ya bukaci gwamnan da yayi murabus, idan ba zai iya magance matsalar tsaro a jihar ba.
