Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Yi Gaba Da Mutane 15 A Asibitin Kutare

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar wasu ?an bindiga sun abka gidajen ma’aikatan asibitin kutare a garin Zaria suka yi awon gaba da mutum 15.

Wani ma’aikacin asibitin ya shaida wa manema labarai cewa mutanen da ?an bindigar suka sace sun ?unshi maza da mata da kuma ?ananan yara.

Ya ce an ?an bindigar sun kai harin ne tsakiyar dare zuwa wayewar safiyar Lahadi.

Wasu rahotanni sun ce cikin mutanen da ?an bindigar suka yi garkuwa da su har da jarirai.

Zuwa yanzu gwamnatin Kaduna da rundunar ?an sandan jihar ba su fitar da sanarwa ba game da harin.

Related posts

Leave a Comment