Rahotanni daga Fadar Shugaban kasa dake birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaba Muhammadu Buhari ya aika tawagar wakilansa domin ganawa da iyalan Sarkin Bichi kan sa ranar daurin auren ‘dansa, Yusuf Buhari, da Zahra Bayero.
An ruwaito cewa wannan tawagar da Buhari ya tura ta hada da gwamnoni, Ministoci, da Dirakta Janar na hukumar DSS, Yusuf Bichi da sauran manyan gwamnati.
An tattaro cewa tuni wasu sun dira jihar Kano da kayayyakin sa rana irinsu goro, da sauransu. Hakazalika an shirya ganawar tawagar da dattijon gidan Bayero, Idris Bayero, da Sarkin Kano, Aminu Bayero, ranar yau Lahadi.
