Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa fataucin miyagun kwayoyi ya haifar da manyan hadurra ga Najeriya fiye da ayyukan ‘yan ta’adda mabambanta.
Shugaba Buhari ya yi wannan bayani ne a ranar 26 ga Yuni, a yayin kaddamar da shirin yaki da miyagun kwayoyi na WADA, da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja.
Shugaban kasar wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Boss Mustapha, ya ce yaki da shan miyagun kwayoyi yaki ne da dole ne a yi shi ba kakkautawa babu sanyin jiki.
“Wannan yakin yafi barkewar tashin hankali da muke da shi a yankin Arewa maso gabashin kasar nan ko ayyukan ‘yan bindiga a yankin Arewa maso yamma ko kuma ayyukan satar mutane da ya wuce misali a dukkan bangarorin kasar nan saboda yaki ne da abinda ke lalata karni uku domin na ga inda kakanni ke shan kwayoyi, iyaye na shan kwayoyi, kuma kari a nan gaba, yaransu na shan kwayoyi.”
Shugaban ya bukaci hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) da ta zakulo dazuzzuka a yankuna daban-daban na kasar don gano inda ake shuka tabar wiwi. Ya umurci hukumar da ke yaki da shan miyagun kwayoyi da ta kassara gwiwar amfani da miyagun kwayoyi tare da hukunta masu sha da masu fataucinsu a kasar.
