2023: Zan Yaki Yunwa Da Rashin Tsaro Idan Na Lashe Zabe – Atiku

?an takarar shugabancin ?asa a PDP, ya yi alwashin fara sauya fasalin Nijeriya daga ranar da ya zama shugaban ?asa a 2023, idan ya yi nasarar lashe za?e.

Wazirin Adamawa ya yi wannan alwashin a Osogbo, babban birnin Jihar Osun, lokacin kamfen ?in PDP a jihar.

Ya ce zai yi amfani da ajandar sa ta sauya fasalin Nijeriya domin ya kawo ?arshen matsalar tsaro yunwa da sauran ?alubalen da ?asar nan ke fama da fuskanta.

Ya ce daga lokacin da aka gama rantsar da shi zai fara aiwatar da ayyukan raya ?asa ta hanyar sake fasalin Nijeriya.

“Babban muradin mu shi ne mu tabbatar mun kawar da dukkan matsalolin rashin tsaro, rarrabuwar kawuna, kawar da danne ha??in tallalin arzikin jama’a da samar da aikin yi ga matasa. Ina ?aukar maku al?awarin cewa tun daga ranar da aka na?a ni shugaba idan na yi nasara a za?en 2023, zan aiwatar da su,” inji Atiku.

Daga nan sai ya ro?i al’ummar jihar Osun su jefa masa ?uri’un su, domin ya cimma burin sa na ceto Najeriya daga mawuyacin halin da ya ce mulkin APC ya jefa ?asar.

“Ba za mu kunyata ku ba, kuma ba za mu ci amanar ku kamar yadda APC ta ci amanar ku ba. Saboda mu na da ?warewa da irin gogewar da Najeriya ke matu?ar bu?ata.”

Gwamna Ademola Adeleke, wanda aka rantsar kwanan nan, ya bayyana Atiku Abubakar a matsayin gogagge kuma mai ?warewar da zai iya ceto Nijeriya, har ya magance matsaloli da ?alubalen da su ka dabaibaye ?asar.

Related posts

Leave a Comment