2023: Zan Sa Wa Kuraye Takunkumi Idan Na Lashe Zabe – Kwankwaso

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ?an takarar shugabancin ?asa a karkashin jam’iyya mai kayan marmari ta NNPP Rabiu Musa Kwankwaso ya halarci wani zama da aka yi da mutane domin bayyana masu manufofinsa a Abuja.

A wannan tattaunawa da Channels TV ta shirya a ranar Lahadi, Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi gwamnonin jihohi da karkatar da dukiyar jihohi. ‘Dan takaran shugaban kasar yace gwamnoni su kan wawuri kudin jama’ansu ta karkashin kasafin tsaro.

Rabi’u Musa Kwankwaso yace a lokacin da yake gwamna a Kano, bai taba karbar wadannan kudi ba. ?an siyasar ya yi alkawarin idan har mulkin Najeriya ya shigo hannunsa, zai dakatar da salon satar a jihohi.

Kwankwaso wanda ya yi gwamna a jihar Kano sau biyu tsakanin 1999 da 2015 yace kudin tsaro da ake ba jihohi bai taimakawa talakawan da ake mulka sai ma ?ara jefa rayuwar talaka cikin matsi da hakan ya haifar.

“A tsawon shekaru takwas da nayi ina Gwamnan jihar Kano ban taba cin ko sisi a cikin kudin tsaro ba, duk da na gaji gwamnatin da tayi imani da wannan. Abin da nayi shi ne na saurari kalubalen rashin tsaro daga bakin Kwamishinan ‘yan sanda, sai na kai maganar zuwa majalisar domin a tattauna a kai.

A ra’ayina kudin tsaro babbar hanya ce ta satar dukiyar ?asa, shiyasa ban karba ba da ina gwamna. Idan na karbi mulki, babu kudin tsaro ga shugaban kasa.”

Related posts

Leave a Comment