Kungiyar tafiyar da harkokin siyasa ta We2gedaNg ta shirya domin ?addamar da shugabannin kungiyar da sauran masu ruwa da tsaki a birnin Kano.
Tsarin wanda aka shirya shi kimanin shekaru biyu da suka gabata, zai amfanar da miliyoyin ‘yan Najeriya ta kafafen ya?a labarai Rediyo da Talabijin da sauran kafafen ya?a labarai na zamani.
A cikin wata sanarwa da ta samu sanya hannun shugaban tafiyar Ibrahim Hussain Abdulkarim yace taron kaddamar da kungiyar zai gudana ne a ranar juma’a 4 ga watan Fabrairu a Bristol Palace Hotel dake Kano da misalin karfe 3 na rana.
Taron wanda zai ha?e kanun dukkanin matasan Najeriya bisa manufa guda, zai taimaka wajen shirin inganta gina ?asa.
Shugaban ya ?ara da cewar We2geda ta ha?a hazikan matasan Najeriya daga dukkanin bangarorin siyasar kasar har da wa?anda ba ‘yan siyasa ba wa?anda ke da buri da kishin gina ?asa.
Abdulkarim ya bukaci ‘yan Najeriya baki ?aya ba tare da banbancin ?abila ko addini ba da su taru su ha?a hannu gaba ?aya wajen ceto Najeriya da ciyar da ita gaba.
Za a ya?a taron kai a tashoshin talabijin na Liberty dake kan Startimes 180, da kuma GOTV a 110, sai Free TV da sauran tashoshin dake tauraron ?an Adam.
