?an takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Ifeanyi Arthur Okowa, ya nuna tsoronsa a game da takarar Peter Obi na Jam’iyyar Labour a zabe mai zuwa.
A zantawarshi da Jaridar Daily Independent Gwamnan na jihar Delta yace Peter Obi abin tsoro ne musamman a yankin kudu maso gabashin Najeriya. Peter Obi ya yi gwamna a jihar Anambra, yanzu yana neman shugaban kasa a inuwar Labour Party.
Ifeanyi Okowa yace inda za a samu matsala shi ne akwai mutanen Kudu da za su zabi Obi domin ya fito daga wurinsu. Ina ma Obi bai fito takara ba “A kudu maso gabas, takarar za ta zama matsala domin ra’ayin mutane da ake samu; amma na san PDP tayi karfi a kudu maso gabas.

[…] Source link […]