Ha?akar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC daga shiyyar arewa maso gabas da shiyyar arewa ta tsakiya sun shawarci shugabannin jam’iyyar da sake duba zabin da aka yi wa Kashim Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa gabanin shekarar za?e ta 2023.
Masu ruwa da tsakin sun kuma bukaci jam’iyyar ta janye nadin da aka yi wa Gwamna Simon Lalong a matsayin Daraktan janar na kungiyar yakin neman zaben Tinubu cikin gaggawa ba tare da ?ata lokaci ba.
A cikin sanarwar da ta fitar a ranar Litinin, 5 ga watan Satumba, sakatare janar na masu ruwa da tsakin, Dauda Yakubu, ya ce tikitin musulmi da musulmi da APC ta yi na janyo rashin jituwa tsakanin mambobinta.
Yakubu ya ce APC tana da dama har zuwa ranar 20 ga watan Satumba, lokacin da INEC za ta fitar da sunayen yan takarar zaben 2023 na karshe, ta duba batun zargin wariya da kiristoci suka ce ana musu.
“Za?en Kashim Shettima da Asiwaju Bola Tinubu ya yi a matsayin abokin takararsa nuna rashin kishi ne da mutunta sauran addinai a Najeriya”.
“Shugabannin hadakar ta arewa maso gabas da arewa ta tsakiya na masu ruwa ta APC tana taro don daukan mataki da zai iya shafar sakamakon zaben shugaban kasa da ke tafe. “Ba boyayyen lamari bane cewa tikitin musulmi da musulmi da jam’iyyar ta yi ya janyo guna-guni a jam’iyyar, musamman arewa ta gabas da arewa ta tsakiya a kasar.
