2023: Kwankwaso Ya Samu Abokin Tarayya A NNPP

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Masanin harkokin masana’antu, Olufemi Ajadi, ya shiga tseren takarar shugaban ?asa a za?en 2023 ?ar?ashin inuwar jam’iyyar NNPP.

Ajadi, shugaban masana’antar ha?a kayan sha, Bullion Neat Global, ya bayyana aniyarsa a Sakatariyar NNPP ta ?asa dake Abuja ranar Alhamis.

Yayin da yake ayyana tsayawa takarar shugabancin kasar Ajadi, ya yi al?awari samar da tsayayyun ofisoshin siyasa a ?asar nan.

“Wannan ce jam’iyya ?aya tilo da take da manufa da irin wacce muke ta yawon nema, ita ce jam’iyyar da ta tara matasan Najeriya wa?anda nake wakilta, da kuma sauran yan Najeriya.”

“NNPP ce ka?ai jam’iyyar da zata share mana fage da kowane ?an Najeriya daga kowane sashi zai sha romon demokara?iyya.” “Saboda haka, ina kira ga matasan Najeriya su shirya su ?aura ?amara, lokaci ya yi da zamu kawo canjin da muke fatan gani a ?asar mu.”

Ajadi ya yi amfani da wannan dama wajen kira da nuna ladabi ga abokan takararsa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Sunday Oginni wanda ke neman takarar gwamna.

Related posts

Leave a Comment