2023: Kanawa Ba Sa Tare Da Kai – Ganduje Ga Amaechi

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ya ?i goyon bayan tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi akan Takarar Shugaban ?asa a Shekarar 2023.

Amaechi ya ziyarci Kano a ranar Laraba a matsayin wani ?angare na neman shawara, gabanin za?en fidda Gwani na shugaban ?asa.

Tsohon Ministan ya ajiye mukaminsa daga cikin ?an Majalisar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari domin neman Takarar Shugaban ?asa a ?ar?ashin Jam’iyar APC.

A taro da masu ruwa da tsaki na ?an Jam’iyyar APC, Ganduje yace Kano Jihar Kano ” Jiha ce mai canje-canje, kuma zata cigaba da haka”.

Ya ?ara dacewa Amaechi zai san inda Jihar ta dosa a lokacin da ya kamata.

Amaechi wanda ya bayyana cewa ?an Jam’iyyar APC tuni suka san inda biyayyar Ganduje ta dosa, yace yazo Kano domin ya canja mashi ra’ayi cewa, yafi kowane ?an Takara cancanta.

Rahotanni sun tabbatar da kusanci da kuma ala?a dake tsakanin Ganduje da jigon Jam’iyyar APC na ?asa Bola Tinubu.

Related posts

Leave a Comment