Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar za?e mai zaman kanta ta kasa, (INEC), ta ce ?aruwar mutanen dake nuna sha’awar tsayawa takarar shugaban ?asa a za?en 2023 ko ka?an ba abin damuwa ba.
Hukumar ta INEC ta ce jam’iyyun siyasa 18 ne kacal halastattun da za su gabatar mata da yan takarar su a takarar shugabancin kasa kuma kowace jam’iyya ?an takara ?aya zata tsayar.
A wata hira da jaridar Leadeship a Abuja ranar Lahadi, Sakataren watsa labarai na shugaban INEC ta ?asa, Rotimi Oyekanmi, ya ce: “Jam’iyyun siyasa 18 ne ka?ai zasu gudanar da za?en fidda gwani, dan haka su ka?ai hukumar zata sanya wa ido.”
Oyekanmi ya bayyana cewa jam’iyyun siyasa ne ke da nauyin shiryawa da gudanar da zaben fitar da ?an takara bisa tanade-tanaden dokokin za?e da tsarin jadawalin INEC. “Saboda haka, idan masu neman kujerar shugaban ?asa suna da yawa, ya wajaba kan jam’iyyun su na siyasa su bi matakan tsayar da mutum ?aya, don haka abun yana kan su ne.”
“Mun yi shirin sa ido a za?en fidda gwani 18 ko abin da bai kai haka ba, ya danganta da jam’iyyun da suka sanar da mu za su gudanar da zaben cikin lokacin da aka ?ayyade.”
