2023: Hukumar DSS Ta Gargadi ‘Yan Takara Kan Labaran Bogi

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS a ta gargadi ‘yan siyasa da su kauce wa yin kalamai marasa tushe yayin da ake kusantar zaben shugaban kasa, wannan na zuwa ne bayan da daraktan yakin neman zaben jam’iyyar APC ya zargi sojoji da dan takarar shugaban kasa na PDP da yunkurin yin juyin mulki.

Hukumar ta DSS ta ce ya zama wajibi jam’iyyun siyasa da masu kula da kafofin yada labaransu su kaurace wa yada labaran karya a lokacin yakin neman zabe da kuma lokacin isar da sakonsu ga magoya bayansu.

Hukumar ta DSS ta ce irin wadannan bayanan marasa tushe na iya janyo martani mai zafi da kuma tada zaune tsaye.

Gargadin na zuwa ne biyo bayan binciken da hukumar ta yi wa daya daga cikin daraktocin yakin neman zaben jam’iyyar APC mai mulki Femi Fani-Kayode.

A shafin Twitter Fani-Kayode ya yi zargin cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar da jami’an tsaro na shirin yin juyin mulki.

Hukumar ta yi wa Fani-Kayode tambayoyi ranar Laraba, sai dai majiyarmu ba ta ji daga hukumar ta DSS ba na game da binciken.

“Hukumar DSS na binciken batun kuma ta kira Fani-Kayode don yi masa tambayoyi, mun zuba ido mu ga yadda zata kaya. Daga zaben jihar Ondo na shekarar 2020, mun ga abubuwa kamar haka. Sojoji suka fito karara suka musanta batun. Amma akwai bukatar a fara yin abubuwan da zasu kawo kwarin gwiwa,” a cewar James a lokacin da ya zanta da wakilin mu.

Related posts

Leave a Comment