Labarin dake shigo mana daga jihar Gombe na bayyana cewar Gwamnan jihar Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, ya roki jama’ar jihar su garzaya su kar?i Katin zabensu domin samun damar ka?a wa APC kuri’unsu a 2023.
Gwamnan yace ?umbin ayyukan da ya zuba a mulkinsa na farko babban alama ce dake nuna dacewarsa musamman yadda ya maida hankali wajen yaye matsin da mutane ke ciki.
Inuwa Yahaya ya yi wannan jawabin ne yayin kamfe a gundumomi 5 da suka ha?a ?aramar hukumar Balanga ta arewa ranar Litinin.
Da farko, gwamnan ya ziyarci fadar Bala Waja, babban Basarake a ?aramar hukumar, Muhammad Danjuma, domin sanar da shi sun zo kamfe a yankin Masarautarsa.
?anjuma ya shaida wa gwamnan cewa ya kwantar da hankalinsa, zai samu kuri’u tuli sakamakon romon ayyukan da ya zuba wa al’umma kamar, “Gina hanyoyi, ?aukar ma’aikata.” A cewar Basaraken, “Yayin ?aukar malaman makaranta na kwanan nan, Balanga ce ta zo na biyu cikin jerin wa?anda suka fi amfana.”
Da yake nasa jawabin, kodinetan kwamitin yakin neman za?en APC a Gombe, Jamil Gwamna, yace PDP zata sha kaye saboda ba abinda ta tsinana wa al’umma a baya. Gwamna ya yi kira ga masu katin za?en su jefa wa APC kuri’unsu tun daga sama har ?asa domin baiwa gwamnati damar ci gaba da ayyukan da ta ?auko a zangon farko.
