Dan gwagwarmaya, Deji Adeyanju, a ranar Laraba ya yi bayani kan yan takarar da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar PDP za su tsayar domin neman shugabancin Najeriya a shekarar 2023.
Adeyanju, ya yi ikirarin cewa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP na duba yuwuwar tsayar da gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto ko gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi.
A wasu jerin bayanai da ya wallafa a shafin Twitter, tsohon mamban na PDP ya yi ikirarin cewa masu ruwa da tsaki a PDP sun gaji da tsayar da Atiku Abubakar takararar shugaban kasa.
Acewarsa, PDP na fushi da Atiku bisa zargin yin watsi da jam’iyyar a zaben shekarar 2015.
Adeyanju ya ce: ” Masu ruwa da tsaki na PDP na son tsayar da Tambuwal ko Bala Mohammed dukkaninsu gwamoni a yanzu a matsayin takarar shugaban kasa tare da dakko wani a kudu a matsayin mataimaki.
“Sun ce kowa ya gaji da mutumin Dubai da Daloli. Me yasa zaku tsayar da shi yanzu? Ina son ganinku a matsayin yan adawa har zuwa shekaru 16.
” Dayawa daga cikinsu na bakin ciki mutumin ya watsar da jam’iyyar bayan zabe tare da komawa kasar Dubai tsawon shekaru 2 amma yanzu ya dawo zai fara yakin neman zaben samun tikiti.
