Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, yace jam’iyyar PDP na da damar lashe za?en shugaban ?asa a 2023, matukar takwaransa na jihar Bauchi, Bala Muhammed, ta tsayar takara, a babban zabe na shekarar 2023 dake tafe.
Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin da yake amsa tambayoyin yan jarida lokacin da ya kai ziyara jihar Bauchi ranar Asabar da ta gabata.
Allah ba zai gafarta wa jam’iyyar PDP ba matukar ta gaza cika burin yan Najeriya na komawa kan mulkin kasa a shekarar 2023 domin ceto ?asar daga durkushewa.
“?an uwana, Bala, na da kwarewa sosai. Ya rike darakta a ma’aikata kacokan, ya zauna kujerar sanata, sannan ya tafi minista kuma yanzun ga shi a matsayin gwamna. Wannan ka?ai ya isa ya zama shugaban ?asa.”
“Sannan idan ka duba abin da yake yi a Bauchi a zangon mulkinsa na farko, ni kaina na zo nan ne na kaddamar da aikinsa, ga takwarorina sun zo yin haka, gwamnoni nawa suka yi haka a zangon farko?”
“Bala ya cancanta ya nemi kujerar shugaban ?asa, ya zarce duk yadda ake tunani. A hange na idan ka duba ala?arsa da sauran mutane babu kamarsa. Dan haka mutane na bukatar ya zama shugaban ?asa ne dan ya cancanta.”
Wike ya koka cewa Najeriya ta tsinci kanta cikin gagarumin rikici saboda rashin tsaro, inda ya kara da cewa lokaci ya yi da PDP zata koma kan madafun iko ta ceto ?asar nan.
