Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El Rufa’i ya nemi a mi?a wa yankin kudancin ?asar mulki a shekarar 2023 bayan wa’adin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.
Mallam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da BBC.
“Idan ka kalli yadda nake, ba na ?aukar mutum yayi aiki tare da ni domin shiyyar da ya fito. Cancanta na ke dubawa, ina duba wanda idan aka ba shi amanar jama’a zai ri?e ta yadda ya kamata.”
Ya kuma ce, “A siyasar da ake yi a Najeriya, akwai tsarin da ake bi na karba-karba, inda kowa ya amince cewa idan arewa ta yi mulki shekara takwas, kudu za ta yi mulki shekara takwas.”
Ya ce duk da ba a rubuta tsarin kar?a-kar?an a tsarin mulki ba, amma kowane ?an siyasa a ?asar ya san da shi.
‘Shi yasa na fito na ce bayan Shugaba Buhari ya yi shekara takwas, ka da wani ?an arewa ya nemi mu?amin. A bar ?an kudu suma su sami shekara takwas.”
Da aka tambaye shi ko da gaske yana da ra’ayin tsayawa takarar shugabancin Najeriya, sai ya ce:
“Ana cewa ina son shugaban ?asa tun ina ministan Abuja, amma ba na so. Wannan shirme ne.”
Ya kuma ci gaba da cewa Allah shi ke bayar da shugabanci, “ko kana so, ko ba ka so yana iya ba ka. Amma ni ban ta?a neman shugabancin Najeriya ba kuma babu wanda zai ce na ta?a nema.”
Batun rufe kasuwannin Kaduna…
Tun da cutar korona ta bayyana a Najeriya, gwamnatoci sun ?auki matakan killace al’umominsu a gida inda har ta kai sun kulle makarantu da wuraren aiki da kasuwanni.
A jihar Kaduna, duk da gwamnatin jihar kaduna ta sassauta matakan kullen da ta saka wa al’umar jihar, har yanzu ba ta bu?e wuraren ibada da kasuwanni da makarantu ba.
Wannan ne ya sa ?an kasuwa ke ?orafe-?orafe kan batun, suna cewa matakin gwamnan jihar na iya kassara su.
Amma gwamnan na Kaduna ya kare kansa daga zargin da ake yi cewa ya ?i tausaya wa ?an kasuwan.
“Su ?an kasuwa suna cewa sun fara bara. Mun ji, amma gara kayi bara kana da rai da ka mutu.”
Ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta bu?e kasuwanni da wuraren ibada ne kawai bayan ta sha ?arfin annobar.
Ya koka da yadda mutane a jihar ba sa kiyaye wa kamar yadda aka bu?ace su.
“Idan muka bu?e masallatai da kasuwanni, cunkoson da muke gani ana yi ?aruwa zai yi ba raguwa ba. Kuma mutum ?aya da ke da cutar na iya ya?a ta ga dubban mutane.”
