?udurorin Shafe Hausawa Da Harshen Hausa – Daga ?ankasawa

Da akwai da?a?den ?udiri na kore samuwar Bahaushe a ?asar Hausa, amman ba da makamai ba. Wannan ?udirin ana aiwatar da shi ne ta hanyar wasa da hankali da rainin wayau ga Bahaushe.

Ga fuskokin wannan ?udirin

  1. Duk sanda Bahaushe ya ce asalin shi Bahaushe ne, sai a jefe shi da maguzanci. Duk wata ?abila a ?asar ga, in mutum ya ce asalin shi daga ita ya ke ba’a cewa komi. Amman da zarar mutum ya ce shi Bahaushe ne, sai ace ashe asalin shi Bamaguje ne. Dubarar ita ce a sa Bahaushen asali ya rin?a tsoron danganta tushen shi da Hausa dan gudun kar a kira shi Bamaguje. Idan Bahaushen asali ya fara danganta asalin shi da Fullanci ko Barbarci ko wani harshen dan gudun kar ace mishi Bamaguje, ai ka ga an kore samuwar Hausawan asali a ?asar Hausa.
  2. Duk sanda Bahaushe ya yi yun?urin wayar da kan ?an uwan shi Hausawa dan su gane ?arerayi da sharrin da ke cikin tatsuniyoyin da ake ya?awa gameda asalin Hausa da Bahaushe, ko dan su ha?a kai su fuskanci inda ke musu ciwo, sai a ce wai ya na ?o?arin raba kan mutane ko kuma kawo ?abilanci. Wani lokaci ma sai ace wai kwangila ya kar?o daga hannun Yahudawa. Dubarar ita ce a hana Hausawa wayar da kan ?an uwan su gameda asalin su dan gudun kar ace su na ?o?arin raba kan mutane, ko kawo ?abilanci ko yan kwangila ne su. Daga lokacin da Hausawa sun ka fara gudun magana kan asalin su ko fuskantar ciwon da ke damun su, daga nan ai an yi nasarar kore asalin Hausawa a ?asar Hausa.
  3. Yun?urin cika harshen Hausa da kalmomin wasu harsunan. Da Turanci zamu iya cewa ana “diluting” harshen Hausa. Ku lura, ba cewa na yi laifi ne Hausa ta aro kalmomi daga wani harshen ba, duk harshen da bai iya aro ya na gab da mutuwa. Amman ga al’ada, harshe na arowa ko kuma ya are kalmomin da ba ya da su ne, ba wa?anda ya ke da su ba. Misali, Bahaushe na da kalmomi irin su “dole” da “tilas”, dan mi ake fifita wajibi da farilla akan su? Hikimar ita ce, a wayi gari Hausar da ake yi ta koma cike da kalmomin aro dan nan gaba a fara ?aryar cewa harshen Hausa ma ?ir?irar shi an ka yi kamar yanda an ka ?ir?iri gur?ataccen Ingilishi “Pidgin English”. Sai a rin?a kafa hujja da cewa wai saboda 80% ?in shi larabci ne, sauran 20% ?in kuma Fullanci da Nufanci da Barbarci da Yarabanci da Zabarmanci ne.
  4. Wani rainin wayau da ake yi ma Bahaushe shi ne idan za’a yi rawa da bazar shi sai ace mishi musulumci ba ruwan shi da ?abilanci. Wannan haka ne. Amma duk inda ka je cikin ?abilu musulmai a duniya, harda ?asashen Larabawa, za ka iske su na rawa da bazar ?abilanci ne wajen warware matsalolin da ke gaban su. Misali, mi ya sa Sarkin Musulmi na Nijeriya ke zaman uban ?ungiyar Fulani ta Miyetti Allah? Ai da da gaske ne, sai ya tsaya a matsayin shi na uban dukkan Musulmai ba na wata ?ungiyar da ta ke?antu da wata ?abila ba. Yanzu da Sarkin Daura ko Sarkin Zazzau Suleja ko Sarkin Gobir ?aya daga cikin su ya ce shi ne uban ?ungiyar da ta ke?antu da Hausawa zalla a Nijeriya ku na jin za’a bar shi ya sha ruwa?

Muddin an ka yi nasarar hana asalin Hausawa danganta kan su da Hausa dan gudun kar a kira su maguzawa, an ka yi nasarar hana Hausawa magana akan tushen su dan gudun kar a ce su na ?o?arin raba kan mutane ko kawo ?abilanci ko sun amso kwangila, sannan an ka surka harshen da wasu harsunan har ya zamanto asalin kalaman harshen sun ?ace sai dai na aro, mi ya rage ga Hausa?

Daga nan kuma wata rana sai a samu wani mugun ya rin?a cewa ai cikin iyawar Danfodiyo ne ya ?ir?iro harshen Hausa dan mabambantan ?abilun da ke cikin Daular Sokoto su samu abun da turawa ke kira “Lingua Franca”. Kar mu mance tarihin yanda Sarkin Sokoto Muhammadu Bello ya sa an ka rin?a tarawa da ?ona littattafan da Malaman ?asar Hausa sun ka rubuta lokacin ya?in Danfodiyo. Wanda ke kirarin jahadi mi zai sa ya ?ona litattafai in ba dan a ?atar da da?a??un tarihai da masanan ?asar Hausa sun ka rubuta ba.

Mu zurfafa tunani ?an uwa.

Related posts

Leave a Comment