?etare: Mai Mata 39 Ya Mutu

Wani mutum a arewa maso gabashin Indiya, wanda ya fi yawan iyali a duniya, ya mutu.

Ziona Chana mai shekaru 76. Iyalinsa sun ce ya yi fama da ciwon suga da hawan jini.

Mista Chana yana da mata 39 da yara 94 da kuma jikoki da yawa.

Ya zauna tare da dukkanin iyalinsa a wani gida bene hawa hudu da ke wani kauye mai tsaunuka a jihar Mizoram, da ke iyaka da Myanmar.

Jami’ai sun ce gidan ya zama wani babban wurin jan hankali ga ‘yan yawon bude ido saboda yawan iyalin mutumin.

Mista Chana ya shugabanci wata kungiyar mabiya addinin Kirista da ke ba da damar auren mata fiye da daya.

Ya fara yin aure yana da shekara 17.

Related posts

Leave a Comment