?etare: Trump Ya Kori Sakataren Tsaronshi

Shugaban Amirka Donald Trump ya kori sakataren tsaron kasar Mark Esper tare da maye gurbinsa da Daraktan cibiyar yaki da ta’addanci na kasar Christopher Miller.

Trump da kan sa, ya sanar da haka a wani sakon twitter da ya wallafa a ranar Litinin, yana mai gode wa Esper kan gudunmuwar da ya ba kasar.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Trump ya ki amincewa da sakamakon zaben kasar, wanda ya sha kaye a hannun Joe Biden.

Dama dai ana yawan samun sabani tsakanin Trump da sakataren tsaron.

Ko a watanni biyar da suka gabata, an samu takin saka tsakaninsu, bayan ya ki amincewa da umarnin Trump na jibge jami’an soji don su tarwatsa masu zanga-zangar Black Lives Matter, wadanda ke yaki da kyamar da ake nuna wa bakar fata.

Haka ma Esper ya yi hannun riga da Trump kan matakinsa ga kungiyar NATO.

ABC News sun ruwaito cewa Trump bai ji dadin hakan ba, wanda ake ganin hakan ta kai ga ya kori sakataren tsaron.

A wani labarin kuma wasu ruhotanni na nuna cewa uwargidan shugaba Trump ta shirya rabuwa da mijin nata jim kadan bayan faduwarsa zaben.

Ku kasance da shafinmu na www.muryaryanci.com domin samun ingantattun ruhotanni da dumi dumin su

Related posts

Leave a Comment