Gwamnantin jihar lagas karkashin jagorancin Babajide Sanwo Olu ta ayyana dokar ta baci a fadin jihar biyo bayan zanga zangar EndSars da taki ci taki cinyewa.
An kwashi kimanin mako biyu kenan da fara zanga zangar lumana a fadin jihar da sauran jihohin kudancin kasar nan ciki da harda babban birnin tarayya abuja. Da farko dai matasan sunfara zanga zangar lumana inda daga bisani gwamnatin tarayya dana jihohi suka amince da bukatun su Amman kuma duk da haka basu janye zanga zangar bama sai sauya salo da sukayi inda suka fara cutar da al’ummar gari da kone konen hukumomin gwamnati.
Biyo wannnan mataki da suka fara dauka nema gwamnatin jihar legas ta sa dokar hana fita a fadin jihar Wanda dokar zaifara aiki yau da misalin karfe 4 na yamma.
Dokar tace masu saida kayayyakin masarufi da sauran ma’aikata na mussamman zasu iya fitowa aiki tare da katin shaida (ID Card) kuma gwamnatin zata hukunta duk Wanda ya saba wannnan doka.
Ko a jiya litinin jaridar Muryar Yanci ta kawo maku ruhoton yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari yace bazai hana matasan kasar nan gudanar da zanga zanga ba Amman suyi shi cikin lumana kuma kar su bari ayi anfani dasu wurin tada tarzoma.
Kuna ganin matakin da gwamnatin jihar legas ta dauka bashi ya kamata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka ba domin kawo karshen wannnan zanga zangar?
