Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamnatin Jihar ta sanya hannu akan dokar hukuncin kisa ga duk wani dan bindigar da aka samu da laifi a jihar, yayin da aka tanadi hukuncin daurin shekaru 20 akan masu taimaka musu da bayanai.
Gwamna Bello Matawalle ya sanya hannu akan wannan sabuwar doka wadda ake sa rai ta taimaka wajen shawo kan matsalolin tsaron da suka mamaye jihar, kuma suke ci gaba da daukar rayuka ba tare da kaukautawa ba.
Dokar na zuwa ne kwana biyu bayan gwamnatin Jihar ta umurci jama’a da su mallaki bindigogi domin kare kan su daga ‘Yan bindigar da suka hana su zaman lafiya.
Gwamnatin tace zata taimakawa jama’a wajen mallakar bindigar bayan tantance su da jami’an tsaro za suyi domin tabbatar da ingancin halayen su.
