Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce za su ci gaba da kai hare-hare Gaza da dukkan karfinsu, duk da kiran da kasashen duniya ke yi na tsagaita wuta. kamar
A wani bayani da ya yi a gaidan talabijin, Benjamin Netanyahu yace za a ci gaba da kai hare-hare ta sama iya karinsu, za kuma kara da cewa za su gasa wa shugabannin Hamas da ke Gaza aya a hannu.
Hare-haren saman da Isra’ila ke kai wa Gaza sun ruguza wasu gine-gine uku tare hallaka mutum 24 kamar yadda hukumomin lafiya a Gaza suka bayyana.
Wannan ne mummunan rikicin da aka gani a kusa tun wanda aka yi a 2014 da ya yi dai-dai da Gaza.
