Wani ?an tauri mai suna Nadabo Alhassan ya gamu da ?acin rana, bayan da ya farke cikinsa da wu?a a yayin bikin ?an tauri.
An ruwaito cewa lamarin ya faru ne a garin Gani, ?aramar Hukumar Sumaila a Jihar Kano a ranar Lahadi.
Tun da farko dai, a yayin bikin na ?an tauri, Alhassan, ?an shekara 40, ya zo ya yi kirari, ya yi kirari, sai kuwa ya ri?a da?awa kan sa wu?a a sassan jikinsa.
An rawaito cewa, a yayin da Alhassan ya rufe idonsa yana ta gabzawa kansa ?arfe, ai kuwa sai abokansa na tauri su ka ri?a cewa “ya isa! ya isa!!”, amma ina, tsumin tauri ya tashi, sai kawai ga tumbin sa a waje.
Kafin ka ce kwabo, Alhassan, ?an asalin garin Keta-bura, ?aramar Hukumar Ningi a Jihar Bauchi, ya fa?i cikin jini shame-shame.
Nan da nan a ka kira ?an sanda, inda su ka bazamo , su ka kuma garzaya da shi asibiti.
Kakakin Rundunar ?an Sanda ta Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni Kwamishinan ?an Sanda, Sama’ila Shu’aibu Dikko ya bada umarnin a garzaya da ?an taurin asibiti.
To amma, duk wannan abun da a ke, Alhassan ya tsallake rijiya da baya, inda kakakin ?an sanda ya tabbatar da cewa yanzu haka yana nan yana kar?ar magani a asibitin Gani da ke Sumaila.
