Shugaban ?asa Ya Nemi Taimakon Sarakuna Wajen Sauke Nauyin Matasa

Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya nemi goyon bayan Sarakunan gargajiya wajen ?o?arin gwamnatinsa na biya wa matasan ?asar bu?atunsu.

Shugaban kasar ya nemi hakan ne a yayin taron da ya yi da masu ri?e da sarautun gargajiyar wanda aka yi a fadarsa da ke Abuja, babban birnin Najeriya ranar Alhamis.

”Mun ji koken-koken matasanmu da ?a?anmu kuma muna duba bu?atunsu,” a cewar Shugaba Buhari.

Ana ganin shugaban ya shirya taron ne bayan da aka shafe makonni biyu matasa a ?asar suna gudanar da zanga-zangar nuna adawa da rundunar ?an sanda mai ya?i da fashi da makami ta Sars.

Matasan sun gabatar da wasu ?arin bu?atun baya ga na rushe Sars wanda gwamnati ta biya musu ta hanyar rushe rundunar, sai dai duk da haka ba su janye daga tituna ba, lamarin da a ?arshe ya riki?e zuwa rikici.

A yayin taron, Shugaba Buhari ya kuma jaddada cewa, ”Domin yin nasara a kan wannan muradi namu, muna son goyon bayanku da amfani da muryarku don taimakawa wajen isar da sa?onmu.

”Kusancinku da mutanen nan ne ya sa kuka fi dacewa da isar musu da sa?on da tabbatar da cewa sun samu martaninmu kuma ya yi tasiri,” a cewar shugaban.

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ?asa Farfesa Ibrahim Gambari ne zai jagoranci manyan jami’an gwamnati zuwa sassan ?asar daban-daban ”inda za su tattauna da ku a wannan aikin. Daga nan zai kawo min rahoto kan ra’ayoyinku,” in ji Buhari.

Shugaba Buhari, ya bayyana rawar da masu sarautun gargajiyar ke takawa a matsayinsu na masu kula da kare martabar al’adu, sannan ya ro?e su da su ri?e amanar da aka dora musu tare da mayar da kowa nasu.

Ana ganin martabar da masu sarautun gargajiya ke da ita a idon al’umma ce ta sa shugaban ?ora musu wannan nauyi.

“Ina son na sake gode muku kan rawar da kuka taka wajen kwantar da hankalin matasa ta hanyar amfani da fasaharsu da kuma cikakken ikon da suke da shi. Idan har kuka tabbatar da zaman lafiya, to kun yi wa ?asar nan babban aiki,” kamar yadda ya ?ara da cewa.

Shugaba Buhari ya kuma yi garga?i cewa gwamnatinsa ba za ta bar kowa ko wace ?ungiya ta yi wa zaman lafiya barazana ko lalata ?o?arinta ba.

Sannan ya ce a yanzu haka ana ?o?arin magance ?ata gari daga cikin rundunar ?an sandan ?asar, tare da kawo sauyi a aikinsu ta hanyar inganta walwalarsu da yanayin aikinsu.

Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ne ya jagoranci tawagar masu sarautun, wadanda suka ha?a da Ooni na Ife, da Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi da Sarkin Kano da Sarkin Fika da Tor na Tiv da shugaban sarakunan gargajiya na jihar Imo da sauran manayan masu sarautun gargajiya daga fa?in ?asar.

Rahoton BBC Hausa

Related posts

Leave a Comment