Rahotanni daga yankin ?aramar Hukumar ?an?ara ta Jihar Katsina na nuni da cewa ayarin wasu iyaye Mata sun gudanar da zanga Zanga-Zangar lumana a garin ?an?ara domin nuna alhini da damuwa akan satar ?aruruwan ?alibai da ‘yan Bindiga suka yi a makarantar kimiyya dake ?an?ara a jihar Katsina a ranar Asabar.
Masu zanga zangar na neman ayi gaggawar ceto daliban da wasu yan bindiga suka yi garkuwa da su a daren ranar Juma’a, 11 ga watan Disamba.
Wata mata wacce ta bayyana kanta a matsayin daya daga cikin iyayen daliban da aka sace ita ce ta jagoranci zanga zangar.
Masu zanga zangar sun kewaye harabar makarantar da wasu yankunan garin dauke da kwalayen sanarwa da sakonni daban-daban kamar irinsu: ‘Ya zama dole gwamnati ta yi magana’, ‘muna so a dawo mana da yaranmu’ da kuma ‘muna son tsaro a Kankara.’
Har ila yau masu zanga zangar na ta wake-waken neman a ceto daliban da aka sace.
A halin da ake ciki, gamayyar kungiyoyin arewa sun yi barazanar tattara dalibai da matasan domin yin zanga zanga a jihar Katsina idan har ba a ceto yaran da aka sace a kan lokaci ba.
Shugaban kungiyar reshen arewa maso yamma, Jamilu Aliyu wanda ya zanta da taron manema labarai a Katsina ya ce: “Mun yi Allah wadai da wannan rashin imanin sannan muna kira ga kama masu laifin cikin gaggawa tare da hukuntasu.
Sannan muna Allah wadai da gazawar gwamnati wajen ba wadannan yaran bayin Allah da basu ji ba basu gani ba kariya daga wannan mummunan hari.
“Idan har gwamnati ta gaza ceto daliban da aka sace cikin dan kankanin lokaci, CNG ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tattara dubban daruruwan dalibai domin ci gaba da zanga zanga, har sai an ceto yaran, koda kuwa za mu rasa ranmu ne.”
Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da rufe dukkanin makarantu a jihar tare da kawo karshen zangon karatu na uku daga ranar Asabar 12 ga watan Disamba.
Har ila yau gwamnati ta umurci dukkanin makarantu kama daga na gwamnati har masu zaman kansu a kan su ci gaba da rufe makaranta har sai baba ta gani.
Wannan sanarwar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar Katsina, Sani Danjuma Suleiman ya fitar kuma aka rarraba ga manema labarai a Katsina.
