Satar Kayan CORONA: An Dam?e Mutane 200 A Adamawa

Rundunan ‘yan sandan jahar Adamawa tace yanzu haka tana tsare da mutane dari biyu da talatin da takwas wadanda ake zargi da aikata laifin diban kayayyakin gwamnati dana jama’a da kuma rashin bin doka.

Kwamishinan yan sandan jihar Adamawa Olubenga Adeyanju ne ya bayyana haka a lokaci da ya yake gabatarwa manema labarai wadanda ake zargin a shelkwatar rundunan dake yola.

Kwamishinan yace an kama wadanda ake zargine bisa tuhumarsu da fasa runbunan adana kayakin abinci gwamnati dana al umma tare kuma da kwashe musu kayakin abinci da dama harma da wasu kayakin dabam dabam.

Cikin kayakin da ake zargin mutanen da sacewa dai sun hada da turoktoci dama kayakin abinci da dama.
Sai rundunan yan sandan tace ta gano turoktoci sittin da hudu kawo yanzu da kuma wasu kayaki da dama.
Harwayau kwamishinan yan sandan yace cikin mutane dari biyu da talatin da kwas, dari da tamanin da hudu sune wadanda ake zargi da sace kayakin gwamnati dana jama a. A yayinda hamsin da hudu kuma ana zargin sune da karya dokan hana fita wanda gwamnatin jahar Adamawa ta sanya a fadin jahar baki daya.
Don haka nema kwamishinan yan sandan ya shawarci matasa dama sauran jama a da su kaucewa duk kanin abinda zai karya doka, dama abinda zai kawo tashin hankali a tsakanin al umma baki daya.

Ku kasance damu a shafin mu na www.muryaryanci.com domin samun ingantattun labarai da dumi dumin su.

Related posts

Leave a Comment