Najeriya Na Mataki Na Biyu ?angaren Cin Hanci Da Rashawa A Afirka

Najeriya ta sauya lamba ta 149 cikin jerin kasashe mafi rashawa a duniya a 2020, bisa alkaluman binciken da Kungiyar Transparency International ta fitar a wannan shekarar.
Najeriya ta samu maki 25 cikin 100.

Transparency International na bada maki ne daga 0 zuwa 100. Sifiri (0) na nufin kasar da tafi rashawa, 100 kuma kasa mara rashawa.

Hakan na nufin cewa rashawa ta kara yawa a Najeriya bana da maki 29, sabanin maki 27 da Najeriya ta samu a 2018.

Bisa Alkaluman, Najeriya ta zama kasa mafi rashawa ta biyu a yammacin Afrika, yayinda kasar Guinea Bissau ta zama kasa mafi rashawa a nahiyar.

A nahiyar Afrika, kasashe 12 kadai suka fi Najeriya rashawa. sune Zimbabwe, Chadi, Eritrea, Burundi, Congo, Guinea Bissau, DC Congo, Libya, Equatorial Guinea, Sudan, Somalia da Sudan ta Kudu.
Kasar Somalia da Sudan ta kudu ne kasashe mafi fama da rashawa a duniya.

Shugaba Buhari ya zama shugaban kasa da yayi alkawarin kawar da rashawa da ta zama annoba na tsawon shekara da shekaru.
Amma tun lokacin da ya zama shugaban kasa, rashawa na kara yawa a kasar.

Related posts

Leave a Comment