Kano: Daya Daga Cikin Malaman Da Suka Yi Mukabala Da AbdulJabbar Ya Rasu

Malam Mas’ud Mas’ud Hotoro, ?aya da ga cikin malaman da su ka jagoranci mukabala da malam Abduljabbar Nasiru Kabara ya rasu.

Jaridar Kano Focus ta ruwaito cewa Malam Mas’ud ya rasu ne a daren jiya Laraba, sakamakon ha?arin mota a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria.

Idan za a iya tunawa malamin na cikin malamai hu?u da su ka yi Mu?abala da Abduljabbar a kwanakin baya.

Malamin shi ne wanda ya wakilci ?angaren ?adiriyya ya yin zaman mu?abalar.

Rahotanni sun baiyana cewa za a yi jana’aizar malamin a yau Alhamis a gidansa da ke Hotoro da karfe 2:00 na rana.

Related posts

Leave a Comment